Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sauke kwamishinansa biyu daga muƙamansu.
Mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Kwamishinonin da abin ya shafa su ne na Ma’aikatar Muhalli, Injiniya Emat Kois, da kuma Kwamishinan Hulɗa da Gwamnatoci da Harkokin Musamman, Honarabul Tukur Ibrahim.
Hakama gwamnan ya sanar da nadin Injiniya Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan a matsayin sabbin kwamishinonin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke.



