Tsohon ɗan wasan gaba na Barcelona, Carles Perez mai shekaru 27, na ci gaba da neman lafiyarsa biyo bayan da kare ya cije shi a gabansa.
Rahotanni sun bayyana cewa ya samu raunin ne yayin da yake ƙoƙarin raba karensa da wani kare a lokacin da suka fara faɗa.
Jaridar The Mirror ta ruwaito cewa an kai shi wani asibiti mai zaman kansa da ke Panorama a kusa da garin Thessaloniki, inda aka yi masa dinki har guda shida a wurin da karen ya cije shi.