Kididdiga ta nuna cewa fiye da mutum miliyan 1.4 da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin Arewa maso Gabas na Nijeriya ke fuskantar barazanar yunwa sakamakon janyewar tallafin agaji daga Majalisar Ɗinkin Duniya.
Rahoton Cadre Harmonisé, wanda gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar FAO, WFP, da sauran kungiyoyin kasa da kasa suka fitar, ya yi hasashen cewa mutane miliyan 33.1 za su shiga matsanancin rashin abinci tsakanin watan Yuni zuwa Agusta 2025, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Saboda haka, jimillar ‘yan Najeriya da ke fuskantar barazanar yunwa ta haura zuwa miliyan 34.7, adadi mafi girma a cikin shekaru da dama, inda akasarin su ke zaune a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, wuraren da rikicin Boko Haram da sauran hare-haren tsaro suka addaba tsawon shekaru.
Ƴan Nijeriya miliyan 34 ke fuskantar barazanar yunwa bayan janye tallafin majalisar dinkin duniya – In ji wani rahoto
-


