Bankin Raya Kasashen Afirka ya amince da bayar da bashi na dala miliyan 46 domin tallafa wa shirin gyaran cibiyoyin lafiya a jihar Sokoto.
A cewar wata sanarwa daga bankin da jaridar Punch ta samu a ranar Juma’a, hukumar gudanarwar bankin ta amince da bashin ne domin magance matsalolin da suka dade suna hana samun ingantaccen kulawar lafiya a yankin.
Bankin ya bayyana cewa tsarin lafiya na jihar na fuskantar gagarumin kalubale, inda alamomi da dama ke nuna gazawa wajen inganci da isar da ayyukan lafiya ga al’umma.
Bankin raya Afrika ya amince da bashin dala miliyan 46 domin gyaran cibiyoyin lafiya a jihar Sokoto
-


