DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Har yanzu akwai masu karbar Naira dubu 4000 a matsayin kudin fansho a Sokoto – Kungiyar tsoffin ma’aikata

-

Tsofaffin ma’aikata a jihar Sokoto sun bayyana takaici kan yadda aka yi watsi da su, tare da bukatar gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa wajen magance halin kunci da suke ciki.

Da yake zantawa da jaridar Punch, Sakataren kungiyar tsofaffin ma’aikatan gwamnati ta jihar Sokoto, Malam Muhammad Garba, ya bayyana cewa tsarin fansho a jihar ya tsaya cak fiye da shekaru ashirin, lamarin da ya jefa dubban tsofaffin ma’aikata cikin talauci duk da tanadin kundin tsarin mulki da ke bukatar karin fansho lokaci-lokaci.

Ya kara da cewa karo na karshe da aka yi karin fansho tun a zamanin gwamnatin Bafarawa ne, inda aka kara kudin fansho zuwa Naira 4,000.

A cewarsa, tsarin fansho na jihar bai sauya ba duk da karin mafi karancin albashi na Naira 18,000, da Naira 30,000, da kuma sabon karin Naira 70,000 da aka aiwatar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara