Watanni goma sha biyu bayan dubban ’yan Nijeriya sun fita kan tituna suna kokawa kan tsananin wahalar rayuwa da rashin shugabanci nagari, masu shirya zanga-zangar #EndBadGovernance da masana tattalin arziki sun ce halin da ake ciki ko dai bai canza ba, ko ma ya kara muni.
Zanga-zangar, wadda ta gudana daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024, ta samo asali ne daga matsin tattalin arziki, hauhawar farashin kayan masarufi, karancin ayyukan yi da hauhawar farashin mai – lamarin da ya fusata ƴan kasar a sassa daban-daban.
Hakama kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana cewa har yanzu gwamnati bata tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe ko aka kama ba.
Rahoton Amnesty ya nuna cewa ’yan sanda sun kashe akalla mutane 24 a lokacin zanga-zangar tsakanin ranar 1 zuwa 10 ga Agusta a jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Borno, Niger da Kaduna.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar kuma an kama su tare da yi musu shari’a bisa tuhumar da ta bayyana da cewa karya ce.
Har ila yau, kungiyar ta Amnesty ta ce ana cigaba da gudanar da shari’u a wasu daga cikin jihohin da abin ya shafa ciki har da Abuja, ba tare da samun wani cikakken adalci ba ga wadanda suka rasa rayukansu ko aka ci zarafinsu.



