Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi da su kara mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’ummar karkara ta hanyar zuba jari a bangarorin da suka shafi kawar da talauci, inganta lantarki, bunkasa noma da gina ababen more rayuwa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) karo na 150 da aka gudanar a fadar shugaban kasa a Abuja, inda ya ce dole ne gwamnoni su hada kai da gwamnatin tarayya domin farfado da tattalin arzikin yankunan karkara.
Ya kuma bukaci a rungumi amfani da injuna a harkokin noma, a yaki matsalar rashin tsaro, sannan a kara shigar da yara makaranta ta hanyar ci gaban shirin ciyar da dalibai a makarantu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkar yaɗa labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya fitar.



