Hukumomi a kasar Brazil sun kaddamar da bincike bayan wata budurwa ‘yar shekara 20 ta rasu kwatsam a cikin wata motar haya, inda daga baya aka gano iPhone guda 26 a lika a jikinta.
Jaridar Daily Mail ta rawaito cewa lamarin ya faru ne yayin take kan hanyar Foz do Iguaçu zuwa birnin São Paulo, sai matashiyar ta fara fuskantar matsalar numfashi.
Yayin da jami’an kiwon lafiya ke kokarin ba ta agaji, sun lura da wasu kumburi a jikinta, wanda hakan ya sa suka bincika sosai.
Daga nan ne aka gano wayoyin iPhone 26 da aka lika da tef a kirjinta da cikinta.
Hukumomi sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin musabbabin mutuwarta.