DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NBC kawai ke da hurumin soke lasisin gidan rediyo – Martanin ministan yada labarai ga Gwamnan Neja

-

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na Nijeriya Mohammed Idris, ya bayyana cewa hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ce kadai ke da ikon janye lasisin kowanne gidan rediyo ko talabijin ba gwamnoni ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani martani kan matakin da gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya dauka na rufe Gidan Rediyon Badeggi FM da kuma umarnin a kwace lasisin aikinsa, bisa zargin yada shirye-shiryen da ke tunzura jama’a da saba ka’idojin aiki.

Google search engine

Matakin ya haifar da cece-kuce da suka daga sassa daban-daban, ciki har da Amnesty International, wadda ta soki gwamnatin jihar bisa tuhumar ta da take hakkin ‘yancin kafafen yada labarai.

Ministan ya bayyana cewa, a tsarin doka, ba wani gwamna ko jami’in gwamnati da ke da ikon rufe kafar yada labarai kai tsaye ko kwace lasisinta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Ministan ya nuna damuwa kan korafe-korafen da gwamnatin ta gabatar dangane da rufe gidan rediyon Badeggi FM.

Ya tabbatar da cewa za a warware lamarin cikin gaskiya da adalci, tare da bin doka da ka’idojin da hukumar da ke kula da gidajen rediyo da talabijin (NBC) ta shimfida.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara