Omoyele Sowore ya ce zai amsa gayyatar ‘yan sandan Nijeriya, duk da cewa ya san wani kokari ne ake na toshe muryarsa.
Fitaccen ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, ya bayyana cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sake gayyatar sa zuwa hedkwatar rundunar da ke Abuja kan zargin yin “jabun takardu da tayar da hankalin jama’a.”
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sowore ya bayyana gayyatar a matsayin wani sabon yunkuri daga IGP Kayode Egbetokun, wanda ya ce ba zai iya jure matsin lamba daga talakawa da ‘yan gwagwarmaya ba.
‘Yan sandan Nijeriya sun bukaci Sowore ya bayyana a ofishinsa bisa zargin sa da hannu wajen aikata laifi
-


