Kungiyar SERAP ta bukaci Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, da ya janye matakin rufe gidan rediyon Badeggi FM, ya dawo da lasisinsa, kuma ya daina barazanar rusa ofishin rediyon.
SERAP ta zargi gwamnatin Bago da keta ’yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin kafafen yada labarai, tana kuma neman a daina gallaza wa mai gidan rediyon, Shuaibu Badeggi, da ma’aikatansa.
A cewar SERAP, rufe rediyon da zargin karya bisa rashin hujja ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa da alkawarin kare ’yancin bil’adama.
Ta ce idan gwamnatin Neja bata dauki mataki cikin awanni 48 ba, za ta dauki matakin shari’a.


