Tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce idan Allah ya ba shi nasara a zaben 2027, zai yi mulki na wa’adin shekara hudu kacal. Obi ya bayyana hakan ne domin nuna cewa dogon zama a mulki ba shi ne ma’aunin nasara ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a jiya, Obi ya yi nuni da manyan shugabanni na duniya kamar Abraham Lincoln, John F. Kennedy da Nelson Mandela, a gajeren lokaci da suka yi a mulki, sun bar tarihi da ci gaba mai ɗorewa.
Obi ya ce manufarsa ita ce shugabanci na gaskiya, cancanta da kafa kyakkyawan tarihi, ba wai yin shekaru da dama a ofis ba.
