Wani jariri namiji da aka haifa a jihar Ohio da ke Amurka, ya zama “jariri mafi tsufa a duniya” bayan an haife shi daga ɗan ciki da aka daskare fiye da shekaru 30 da suka gabata.
Jaririn mai suna Thaddeus Daniel Pierce an haife shi ne a ranar 26 ga Yuli ta hanyar dashen ciki na IVF da ma’auratan Lindsey da Tim Pierce daga birnin London, Ohio, suka yi ta hanyar ɗaukar ciki daga wata asibiti.
Rahoton MIT Technology Review ya bayyana cewa an daskarar da ɗan cikin tun watan Mayun shekarar 1994.
Lindsey ta bayyana cewa mijinta, Tim mai shekaru 35, yana ƙaramin yaro ne lokacin da aka kirkiri ɗan cikin da yanzu ya zama ɗansu.