DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bayo Ojulari ya halarci wani taro yayin da ake cece-kucen ya sauka daga shugabancin NNPCL

-

Shugaban kamfanin man fetur na ƙasa, NNPCL Bayo Ojulari, wanda ake jita-jitar an sauke shi daga mukami, ya bayyana a wani taron da ƙungiyar injiniyoyin man fetur ta shirya a birnin Lagos a ranar Litinin.

A wani faifan bidiyo da wasu mahalarta taron suka tura wa jaridar Daily Trust, an ga Ojulari yana gabatar da jawabi ta hanyar Zoo), kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan baki na taron.

A baya-bayan nan dai ana ta rade-radin cewa an sauke Ojulari daga kujerarsa ta shugabancin NNPCL, sai dai, babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban ƙasa ko daga kamfanin NNPCL kan wannan batu.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara