Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa kowacce ‘yar wasan ƙungiyar kwallon kwando ta mata ta D’Tigress, kyautar dala 100,000 bayan nasarar da suka samu a gasar AfroBasket.
An sanar da hakan ne a wani taron tarbar nasara da aka shirya a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, inda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaban Ƙasa a wajen bikin.
Shugaban ya yaba da bajintar ‘yan wasan da suka sanya sunan Nijeriya a mataki na duniya, tare da nuna cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa wasanni, musamman ma mata.
Matar shugaban kasa Oluremi Tinubu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, da wasu jami’ai ne suka tarbi tawagar D’Tigress da mai horaswa Rena Wakama.
D’Tigress ta doke Mali da ci 78–64 a wasan ƙarshe da aka buga a kasar Côte d’Ivoire ranar Lahadi, inda suka lashe kofin kwallon kwandon mata na Afrika wato AfroBasket karo na bakwai kuma karo na biyar a jere.
Wannan karramawar ta zo ne mako guda bayan da Shugaba Tinubu ya karrama ƙungiyar Super Falcons da dala 100,000 kowacce, bayan nasarar lashe gasar WAFCON karo na 10 a Morocco, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce da martani daga ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta.



