Wasu tsoffin sojojin Nijeriya da suka ajiye aikin soja da yardarsu sun gudanar da zanga-zanga a gaban hedikwatar ma’aikatar kuɗi ta kasa a Abuja a ranar Litinin, inda suka rufe babbar ƙofar shiga ginin.
Zanga-zangar, wadda ta fara misalin ƙarfe 10:15 na safe, ta samu halartar jami’an tsaro da dama daga ɓangarorin sojoji, ‘yan sanda da kuma Hukumar DSS, domin hana barkewar rikici da kare dukiyoyin gwamnati.
Yayin da yake magana da Daily Trust, ɗaya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, Staff Sergeant Simon Ipwu, ya bayyana cewa rashin biyan su kuɗaɗen alawus na ajiye aiki da inshora ne manyan dalilan da suka tilasta musu fita zanga-zanga.
Ya ce sun gaji da alkawuran gwamnati, kuma suna buƙatar a biya su hakkokinsu domin su rayu cikin mutunci.


