DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Femi Falana ya caccaki manufofin tattalin arzikin Tinubu

-

Lauyan da ke kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya caccaki matakan tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, yana mai cewa manufofin “tsauraran tsarin ‘neoliberal'” na gwamnatin sun shafe matsakaicin ajin al’umma tare da kara jefa miliyoyin ‘yan kasa cikin talauci.

Falana ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan furucin Shugaba Tinubu na cewa yana sane da mawuyacin halin tattalin arzikin da jama’a ke ciki.

Google search engine

Sai dai Falana ya ce maimakon sauƙa, matakan gwamnati sun kara tsananta wahala da fatara kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ambato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara