DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An faɗi jarabawar WAEC ta bana fiye da shekaru 5 da suka gabata – Daily Trust

-

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta yammacin Afirka (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE na shekarar 2025, inda aka samu gagarumar faduwar dalibai.

Daga cikin dalibai 1,969,313 da suka zauna jarabawar, dubu 754,545 ne kawai suka samu maki mai kyau aƙalla a darussa 5 da suka haɗa da Turanci da Lissafi, wanda ke nuni da kashi 38.32 cikin 100 ne kacal suka samu nasarar.

Google search engine

Shugaban ofishin WAEC a Najeriya, Amos Dangut, ya bayyana cewa an samu raguwa da kashi 33.8% idan aka kwatanta da sakamakon daliban da suka zauna jarrabawar a shekarun baya.

1 COMMENT

  1. Da fatan kuna lafiya, gaskiya sakamakon jarabawa daga jamb zuwa waec na bana ya kara tabbatar da tabarbarewar harkar ilimi a Nigeria, musamman bangaren makarantun gwamnati, la’akari da masu fadiwa ta bangaren su, hakan kuma yana nuni kan ana so a gigita makarantun kudi na yaya masu hanu da shuni ne, a bar ya’yan talakawa kara zube ta bangaren ilimi sai dai muce Allah ya kyauta, ina godiya ku huta lafiya daga naku mai sauraron ku ya da kullum Ayuba Aufu Michika

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara