Shugaban ‘yan bindigar da ake zargi da kai hare-hare a Zamfara, Bello Turji, ya sako mutane 32 da ya yi garkuwa da su tare da amincewa da daina kai wa manoma hari.
Wannan na zuwa ne bayan jerin zama da aka yi har sau uku da wasu malamai a dajin Fakai da ke yankin karamar hukumar Shinkafi, a watan Yuli.
Ganawar da rahoton jaridar Premium Times ya ce malamin addinin misulinci a Nijeriya sheik Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, shi ne ya bayyana a wani taron addini a Kaduna.
Ya ce bayan tattaunawar, Turji ya mika wasu daga cikin makaman da ke hannunsa.
Malamin ya ce ganawar ta biyo bayan roƙon da al’ummar Shinkafi suka yi domin su samu damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.



