Fitattun ‘yan kwallon kafar Afirka da suka hada da Samuel Eto’o na kasar Kamaru da Rigobert Song da Emmanuel Adebayor na kasar Togo da Jay Jay Okocha na Nijeriya ne suka halarci bikin bude gasar.
Tun da farko dai an rufe filin wasan ne bayan da hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta bayyana cewa bai dace da filin wasa na kasa da kasa ba saboda rashin inganci.
An yi gyare-gyaren dala miliyan 300, wanda ya mayar da shi filin wasanni na duniya wanda yanzu ya cika cika ka’idojin CAF da FIFA.