Kasar Ghana ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga ranar Alhamis 7 ga watan Agusta, biyo bayan wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi sanadin mutuwar mutane takwas, ciki har da ministan tsaro Edward Omane Boamah da ministan muhalli Ibrahim Murtala Muhammed.
Shugaba John Mahama na kasar Ghana ya ba da umarnin sassauto da tutocin kasar har zuwa wani lokaci.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Ghana da sojojin Ghana sun fara gudanar da binciken gano musabbabin abinda ya faru kan hadarin.