By Salamatu Alhassan Musa
Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya da haraji ya bayyana damuwa kan ci gaba da rufe wasu iyakokin ƙasar.
Shugaban kwamitin, Leke Abejide, ya ce ci gaba da rufe iyakokin ba ya amfani ga tattalin arzikin ƙasar, inda ya bayyana cewa Nijeriya na asarar kuɗaɗen shiga masu yawa sakamakon wannan rufewar.
Ya yi wannan bayani ne a Kaduna yayin da ya jagoranci wasu daga cikin mambobin kwamitin a ziyarar gani da ido a Yankin Zone B na hukumar Kwastan ta Nijeriya, da ya ƙunshi jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Neja, Kogi, Kwara da kuma Birnin Tarayya Abuja.
Abejide, wanda ya kuma tabo bukatar haɗin gwiwar jami’an tsaro domin dakile matsalar rashin tsaro da ke ƙara shafar samun kuɗaɗen shiga a yankin, inda ya ce kwamitin zai ɗauki matakin gabatar da kudiri a zauren majalisa bayan komawarsu daga hutu na shekara.
Ya ce kudirin zai kasance tare da haɗin gwiwar sauran kwamitocin da ke da alaka da harkokin tsaro, tare da yiwuwar haɗa hannu da takwarorinsu na majalisar dattawa, domin nemo mafita ta dindindin.