Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana dalilanta na cafke dan fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, biyo bayan sahihan zarge-zarge na jabun takardu, cin zarafi ta yanar gizo (cyberstalking) da wasu laifuka da ake bincike akai.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Olumuyiwa Adejobi, ya ce an kama Sowore cikin bin doka da kare haƙƙin wanda ake zargi, sannan aka sake shi bisa beli cikin awanni 48 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya kuma ruwaito ‘yan sandan sun karyata zargin azabtar da shi a Yayin da yake tsare, inda suka ce sun yi la’akari da dokar hana azabtarwa ta 2017 da ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan adam na duniya.



