Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin mafi ƙarfi da dacewa da zama ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2027, yana mai kira ga jam’iyyar ta yi ƙoƙarin dawo da shi.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya ambato Sule Lamido na buga misalin yadda Jonathan ya shugabanci Nijeriya cikin kwarewa da iya mulki, kuma yana iya aiki da kowa.
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan jam’iyyar daga Kudanci a yanzu da zai iya kaiwa matakin gogewar Jonathan da zai samu tikitin takara a jam’iyyarsu ta PDP.
Ya jaddada cewa idan PDP za ta bai wa Kudanci takarar shugabancin ƙasa, babu wanda zai iya fafatawa da Jonathan wajen cancanta, gogewa, da iya sauraron ra’ayoyin jama’a.




Comment:gaskiya nima inada ra’ayin tsohon shugaban kasa najam’iyar P.D.P dommin akudanci shiyayi magakalar tasa rawa fata allah yayimana xabi da alkairi.