Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bukaci a kori ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, da tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, da sauran ‘yan jam’iyyar PDP da suka yi wa APC kamfen a zaɓen 2023.
Lamido, ya yi wannan magana ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya ce lokaci ya yi da shugabancin PDP zai ɗauki matakin ladabtarwa kan ‘yan jam’iyyar da ke cin amanar jam’iyya, yana mai zargin su da shirye-shiryen sake goyon bayan APC a 2027.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda rashin ladabtar ‘yan jam’iyya ke ci gaba da zama al’ada tun bayan taron fidda gwani na 2022.



