Tsohon Ministan Noma da Cigaban Karkara, Cif Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta 2025, yana da shekaru 78 a Duniya.
A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun bayyana cewa marigayin ya rasu ba tare da wata jinya ba, ya kuma bar tarihin gaskiya, rikon amana, da sadaukarwa ga ƙasa da al’umma. Sun ce Ogbeh ya shafe rayuwarsa yana bautawa ƙasa da bayar da gudummawa mai muhimmanci ga ci gaban al’umma.
Jaridar Punch ta ambato iyalan mamacin na godiya ga duk masu yi musu ta’aziyya, tare da sanar da cewa za a bayyana cikakkun shirye-shiryen jana’iza a nan gaba. Sun kuma roƙi a basu damar yin jimami cikin sirri a wannan lokaci na rashin makusanci da aka yi.



