Uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da tallafin Naira miliyan 110 ga iyalan ‘yan wasan Kano 22 da suka rasu a mummunan hatsarin mota a watan Mayu.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce kowane iyali ya samu Naira miliyan 5 ta hannun Victim Support Fund, wani shiri na gwamnati da ke taimaka wa waɗanda suka shiga cikin bala’i da matsanancin hali.
Fadar shugaban ƙasa ta ce wannan taimako na cikin shirin gidauniyar Renewed Hope na shugaban ƙasa Bola Tinubu, tare da nuna tausayawa da kulawa daga tsagin jagoranci.
‘Yan wasan sun rasu ne a kan hanyar Kano–Kaduna yayin dawowa daga gasar National Sports Festival a jihar Ogun.



