Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya dakatar da shirin karbar katin zama mamba na jam’iyyar ADC, yayin da ake rade-radin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na iya shiga takarar shugaban kasa a 2027 tare da neman goyon bayan jam’iyyar.
Atiku, wanda ya fice daga PDP bayan rikice-rikicen cikin gida, ya shirya karbar katin a mazabarsa ta Jada, Adamawa, a ranar 6 ga Agusta, amma an dage taron ba tare da saka sabon lokaci ba.
Shugaban ADC na Adamawa, Shehu Yohana, ya ce Atiku na jiran wasu gwamnoni daga APC su koma ADC kafin a gudanar da muhimmin taron.
Sai dai jaridar Punch ta ce wasu jiga-jigan ADC sun nuna jinkirin na iya zama saboda takaddama tsakanin Atiku da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, wanda ake zargin ya mamaye tsarin jam’iyyar a Kudu.
Sun kuma yi hasashen cewa idan lamarin bai tafi yadda Atiku ke so ba, zai iya komawa jam’iyyar SDP.