An yi imanin cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga mukaminsa saboda dalilai uku da suka shafi rikicin siyasa da matsin lamba daga bangarori daban-daban.
Majiyoyi sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa, dalili na farko shi ne kokarin janyo tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jam’iyyar APC, inda aka bukaci Ganduje da ya hakura da mukaminsa tare da alkawarin samun wani babban matsayi a gaba.
Dalili na biyu kuwa ya shafi rade-radin samun sabani tsakaninsa da fadar shugaban kasa, wanda ya haifar da matsin lamba da ya sa ya sauka daga mukaminsa.
Dalili na uku kuma shi ne bukatar kwantar da hankalin ƴan yankin Arewa ta Tsakiya, waɗanda ke neman rike wannan kujera tun bayan saukar tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu.
Wata majiya ta kusa da Ganduje ta ce matsalarsa ta fara ne lokacin da aka umarce shi ya yi sasanci da tsohon ubangidansa kuma abokin adawarsa a siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso — wanda rikicin siyasa tsakaninsu ya yi tsanani a baya.
Duk da rashin jin dadin wannan mataki, an ce Ganduje ya yi kokarin shawo kan lamarin, yana fatan daga baya zai iya jawo hankalin shugaban kasa zuwa gare shi.
Rahotanni sun kuma nuna cewa fadar shugaban kasa na ganin Kwankwaso ne ke da tasiri da mafi rinjaye a Kano, wanda zai iya taimakawa jam’iyyar a zaben 2027.
Sai dai rashin jituwa tsakaninsa da Ganduje na iya zama cikas ga shigar Kwankwaso cikin jam’iyyar, tare da yiwuwar haifar da sabbin rikice-rikice kan jagorancin APC a jihar.
Tunibu ayi dai muga ni ba dai kwankwaso bane aci dadi lafiya amma fa kasa ni atiku ma bai iya dashi ba bare kai