DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An kai hari kauyuka 15 a Zamfara, an yi garkuwa da mutum sama da dari cikin mako guda – Zamfara circle community Initiative 

-

Sabbin bayanai na nuni da cewa an kai hare-hare a kauyuka 15 da ke jihar Zamfara, tsakanin ranakun 4 zuwa 10 ga watan Agustan 2025.

A wani rahoto da kungiyar Zamfara Circle Community Initiative ta fitar, hare-haren sun kai ga yin garkuwa da mutane 144, da kashe wasu 24, tare da jikkata wasu mutane 16 a wasu kananan hukumomi da dama.

Google search engine

Al’umomin da abin ya shafa sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo a karamar hukumar Bakura.

A karamar hukumar Tsafe, an kai hare-haren a Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils.

Karamar hukumar Mafara an samu labarin hare-haren a Tabkin Rama, Matsafa, da Ruwan Gizo, yayin da Rafin Jema a Gummi da Adabka da masu a Bukkuyum.

Kungiyar Zamfara Circle Community Initiative ta lura da cewa ci gaba da kai hare-hare na nuni da cewa akwai bukatar a dauki matakan tsaro cikin gaggawa domin kare al’umomin da ke karkara daga hare-haren ‘yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara