Rahoton jaridar Punch ya tattaro cewa matatar mai ta Dangote da ke Legas tana samun yawancin danyen man da take sarrafawa daga Amurka, yayin da matatun mai na Indiya ke siyan mai daga Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin Indian Oil ya sayi ganga miliyan daya ta danyen man Agbami daga Najeriya wanda zai isa a watan Satumba, yayin da BPCL ta kuma kulla yarjejeniyar siyan ganga miliyan biyu na man Najeriya har zuwa watan Satumba da Oktoba.
Sai dai, kididdigar Kpler ta nuna cewa a watan Yuli, kaso 60 cikin 100 na man da matatar Dangote ta shigo dashi daga Amurka ne da kiyasin gangar dubu 370 a rana, yayin da kaso 40 cikin 100 ya zama daga Najeriya.
A baya dai, Dangote ya bayyana cewa matsalar samun wadataccen danyen mai daga cikin gida na daga cikin dalilan da suka sa yake dogaro da shigo da na waje.



