Hukumar gudanarwar Ibom Air ta ce wata mata mai suna Comfort Emmanson ta tada rikici a jirgin da ya taso daga Uyo zuwa Legas bayan ta ki kashe wayarta duk da umarnin da ma’aikatan jirgi suka yi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, bayan jirgi ya sauka a Legas, ta kai wa Purser hari, ta taka kafafunta, sannan ta yi amfani da kwalbar kashe wuta a matsayin makami, ta kuma mari jami’an tsaro har ma da manajan filin jirgi.
Tuni dai Jami’an hukumar kula da harkokin Jiragen saman Nijeriya FAAN suka kama ta suka mika wa ‘yan sanda.
Kodaidai Kamfanin jirgin ya ce an haramta mata hawa duk wani jirginsu kuma sun mika rahoto ga NCAA, tare da jaddada manufarsu ta rashin lamuntar duk wani tashin hankali a jirginsu nan gaba.



