Rahoton jaridar Daily Trust ya ce karamar hukumar Safana a jihar Katsina ta shiga yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar yadda Jibia, Batsari, da Danmusa suka riga suka yi, domin kawo karshen hare-hare a yankin.
Taron sulhun ya gudana a bakin dajin Gimi, Runka, karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Abdullahi Sani Safana, tare da Yariman Katsina, Alhaji Sada Rufa’i, da sauran shugabannin gargajiya.
Bangarorin biyu sun amince da janye rikici da gaba a tsakani, tare da bada damar yin noma da walwala ba tare da tsangwamar kowa ba.
Sharuɗɗan yarjejeniyar sun haɗa da dakatar da hare-hare, daukar rayuka, da sace mutane, da kuma bai wa makiyaya damar zuwa kasuwa, asibiti, da sauran wuraren hidima ba tare da cin zarafi ba.



