DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kara wa’adin fara hukunta masu karya dokar amfani da gilashin mota mai duhu

-

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya kara wa’adin fara hukunta masu amfani da gilashin mota mai duhu ba tare da lasisi ba har zuwa 2 ga Oktoba.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito mai magana da yawun ’yan sanda na kasa, DCP Olumuyiwa Adejobi na cewa karin lokacin ya biyo bayan yawaitar neman lasisin ta shafin yanar gizo na hukumar, wanda ke nuna karuwar bin doka daga jama’a.

Google search engine

Ya bayyana cewa karin wa’adin zai bai wa hukumomi damar tantance masu nema sosai, da kuma ci gaba da inganta tsarin tantancewa na yanar gizo da na zahiri, domin tabbatar da sahihancin lasisin da kuma hana kaucewa ka’ida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara