Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a a Nijeriya, Mohammed Idris Malagi ya ce tattalin arzikin Najeriya yana samun habbaka da yabo daga manyan cibiyoyin kimanta tattalin arziki na duniya, abin da ke nuna ƙarin amincewa da alkiblar tattalin arzikin ƙasar.
Ya bayyana haka ne bayan ganawa da Gwamnan Imo kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodimma, a Abuja.
Muhammad Idris ya ce tsare-tsaren tattalin arzikin na shugaba Bola Tinubu sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda rahotanni daga hukumomin ƙasa da ƙasa ke nuna kyakkyawan ci gaba a gyaran tattalin arziki da aiwatar da manufofin gwamnati.
Rahoton Daily Nigerian ya Ambato ministan na cewa, duk da cewa ba a kai ƙarshe ba, an riga an kafa hanyar da za ta kai ga cimma manufofin gwamnati, kuma kafin Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na farko, fa’idodin waɗannan gyare-gyare za su bayyana ga ‘yan ƙasa.
https://shorturl.fm/LLqVn