Shugaban hukumar da ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa tu’annati EFCC, Ola Olukoyede, ya ce wasu ‘yan siyasa na amfani da dabara ta bayyana kadarorin da ba su mallaka ba kafin su hau mulki, domin su kauce wa binciken rashawa.
Wannan ya biyo bayan wani taro na kaddamar da kayan aiki na yanar gizo kan dokokin ma’aikatan gwamnati a Abuja, wanda Olukoyede ya bayyana cewa bincike ya gano wani babban jami’i ya saka adireshin gida daban a takardun bayyana kadarori, duk da cewa gidan bai wanzu ba a zahirance.
Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro yadda daga baya aka gano cewa bayan lashe zabe, jami’in ya gina kadarar a wani adreshi na daban, wanda ya dace da wanda yake nufi tun farko.
Wannan dabara, in ji shi, ana kiranta da “anticipatory declaration of assets” wato bayyana kadarorin da ake shirin mallaka nan gaba.