Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon watanni uku saboda zargin saba wa doka, yin almundahana da karkatar da kudade da kansilolinsa suka gabatar.
Dakatarwar ta biyo bayan rahoton wucin gadi na kwamitin karɓar koke-koke na majalisa, karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa ya gabatar.
Majalisar ta umarci ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta nada mataimakin shugaban karamar hukumar a matsayin mukaddashin shugaban har sai an kammala bincike, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya sanar.
https://shorturl.fm/le5e8