Ministan da ke kula da harkokin tattalin arzikin teku a Najeriya, Adegboyega Oyetola, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin cefanar da tashar jiragen ruwa ta Baro da ke Jihar Neja ga ‘yan kasuwa, domin farfaɗo da ita.
Ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke nazarin kalubale da damar farfado da tashar, inda ya ce tun bayan kaddamar da ita a 2019 ba ta yi aiki yadda ya kamata ba saboda rashin hanyoyin mota, layin dogo da matsalar zurfin ruwa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Oyetola ya ce akwai buƙatar sake zurfafa kogin da haɗa tashar da hanyoyi jirgin kasa, amma rashin kuɗi ya takaita aikin.
Ya bayyana cewa gwamnati na aiki tare da ma’aikatun ayyuka da sufuri, tare da shirin jawo hankalin masu zuba jari na musamman domin cefanar da ita.