Tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya Peter Obi a zaben 2023 karkashin tutar jam’iyyar Leba ya yi kakkausar suka ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ziyara zuwa ƙasashen Japan da Brazil.
Obi ya bayyana damuwa kan cewa tafiyar Tinubun na zuwa ne a lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin tsaro, talauci, da koma-bayan tattalin arziƙi, yana mai cewa shugaba Tinubu na kauce wa kai ziyara jihohin da ke cikin matsala.
Ya kuma ce ya kamata shugaban ya fi yin aiki a cikin gida domin fahimtar halin da ‘yan ƙasa ke ciki, maimakon yin dogayen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.
Obi ya yi kira ga shugaban na Najeriya da ya rage yawan yawace-yawace, musamman inda taron da zai halarta na ƙasashen waje za a iya kammala shi cikin ‘yan kwanaki.
A cewarsa, Najeriya na bukatar jagora mai jajircewa da zai nuna kashi 100 bisa 100 wajen magance matsalolin ƙasar.



