Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa kasashen Japan da Brazil domin halartar taro da kuma ziyarar aiki.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga, Tinubu zai fara tsayawa a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ya wuce Japan.
Shugaban kasar zai halarci taron kasa da kasa karo na 9 kan cigaban Afirka (TICAD9) a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta, za a gudanar da taron ne domin tattauna batutuwan cigaban Afirka, inda Tinubu zai shiga zaman tattaunawar kuma zai gana da shugabannin kamfanoni masu zuba jari daga Japan a Najeriya.
Bayan kammala taron, shugaban Najeriya zai wuce Brazil daga ranar Lahadi 24 zuwa Litinin 25 ga watan Agusta, bisa gayyatar shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.