Wata motar safa ta kamfanin STM na Nijar ta afka cikin cikin wani kogi a kasar Bénin a yayin da take kan hanyar ta ta zuwa babban birnin Yamai na jamhuriyar Nijar bayan ta huto daga birnin Lomé na Togo.
Sanarwar ma’aikatar cikin gidan Bénin ta ce da misalin karfe 12 na daren Lahadi ne hatsarin ya auku inda motar mai dauke da fasinjoji 54 ta kwace daga hannun direban ta je ta daki karfen kariya na kan gada kaifin daga bisani ta fada cikin ruwan na kogin Ouémé.
Hukumomin kasar Bénin sun ce mutum daya ya rasa ransa, sun yi nasarar ceto mutum 9 kuma tuni aka kaisu asibiti yayin da sauran 44 suka ce ana cigaba da neman su a cikin ruwan.







