Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutum 62 da aka yi garkuwa da su sun kubuta, biyo bayan luguden wuta da rundunar sojin sama ta kai a sansanin fitaccen jagoran yan bindiga Muhammadu Fulani, a karamar hukumar Dan-Musa.
Kwamishinan tsaro na cikin gida Dr Nasir Mu’azu ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa luguden wutar sojin saman ya kai ga yankin Jigawa Sawai, da ke kan iyakar Katsina da Zamfara
Dr Nasir Mu’azu yace daga cikin mutanen da suka kubuta, mutum 12 suna samun kulawar likitoci a Asibitin Gwamnati dake Matazu, yayin da wasu 16 ke tare da sojojin Najeriya a Kaiga Malamai.
