Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya NCAA ta bayyana cewa duk fasinjoji a Najeriya dole su kashe wayoyinsu gaba ɗaya a yayin tashin jirgi da sauka.
Shugaban hukumar ta NCAA, Chris Najomo, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce daga yanzu babu sauran amfani da “flight mode” a yayin tashin jirgi.
Rahoton jaridar Daily Nigerian ya ce umarnin ya biyo bayan takaddama tsakanin wata fasinja, Comfort Emmanson, da ma’aikaciyar jirgin Ibom Air, wacce ta jawo cece-kuce a filin jirgin saman Legas a kwanan nan.
Najomo ya ce wannan mataki zai kawo ƙarshen sabanin dokokin da kamfanonin jiragen sama ke bayarwa, tare da tabbatar da tsaro da daidaito a harkar tashi da saukar jiragen a kasar.