Wani bincike da Oxford Policy Management ta gudanar ya nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, akalla dalibai 330 aka sace a kananan hukumomi uku na jihar Katsina – Batsari, Faskari da Kankara.
Hadiza Tijani, wata masaniya daga Oxford Policy Management, ce ta bayyana haka a taron gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar tare da goyon bayan UNICEF da ma’aikatar Ilimi ta Katsina.
Rahoton ya nuna cewa dalibai biyu aka kashe a wannan lokaci, haka kuma ma’aikatan makarantu 15 aka sace, biyar kuma aka kashe. A Kankara kadai, sama da dalibai 300 aka yi garkuwa da su.



