Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta sanya tsohon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL, Mele Kyari, a jerin wayanda za ta sawa ido, kan binciken da ake yi masa kan batun dala biliyan 7.2 da aka ware domin gyaran matatun mai na ƙasar.
Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin rufe wasu asusun banki guda huɗu da ake alakanta da Kyari, bayan tuhumar aikata almundahana.
Majiyoyi daga EFCC sunce za a gayyaci Kyari domin amsa tambayoyi, duk da cewa an sanya shi cikin jerin wa’yanda za ta rika sawa ido.



