Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barrister Sa’idu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar karɓar korafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano PCACC.
An gudanar da rantsuwar ne a gidan gwamnatin Kano, karkashin jagorancin kwamishinan shari’a na jihar, Barrister Haruna Isa Dederi.
Tun da farko, Gwamnan Kanon ya miƙa sunan Barrister Sa’idu Yahya ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin sabon shugaban hukumar.
Barrister Sa’idu Yahaya ƙwararren masani ne a fannin yaƙi da cin hanci, inda ya shafe sama da shekaru 18 yana aiki a hukumar ICPC, musamman wajen bincike da bin diddigin kadarori.



