Hukumar zaben Nijeriya INEC ta bayyana ranar Alhamis, 21 ga Agusta, 2025 domin gudanar da zaɓen cike gurbin zagaye na biyu na majalisar jiha a Kaura Namoda South da ke Jihar Zamfara.
Wannan mataki ya biyo bayan zaɓen cike gurbin da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, wanda jami’in tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Lawal Sa’adu daga Jami’ar Tarayya, Gusau, ya ayyana a matsayin wanda bai kammala ba wato “inconclusive”.
Wannan ya faru ne sakamakon soke kuri’un da aka kada a rumfunan zaɓe guda biyar da ke cikin mazabun Sakajiki da Kembarawa.
Farfesa Sa’adu ya bayyana cewa tazarar kuri’u tsakanin jam’iyyar APC da ke kan gaba da PDP mai biye mata ba ta kai adadin masu katin zaben da aka tattara daga wuraren da aka soke zaɓen ba,wannan ya sa aka tilasta shirya sabon zaben karo na biyu.