DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta ba da belin mutanen da ake zargi da ajalin ‘yan daurin aure daga Zaria zuwa jihar Plateau 

-

Kotun Jihar Filato mai lamba 7 ta bayar da belin mutane 20 da ake zargi da hannu a halaka mutane 13 da suka halarci biki a kauyen Mangun, karamar hukumar Mangu na jihar.

An ba da belin ne a ranar Alhamis, inda mai shari’a Nafisa Lawal Musa ta saurari roƙon lauyan wadanda ake tuhuma, Barista Garba Pwul SAN.

Google search engine

An gano cewa wadanda abin ya faru da su, an halaka su ne a ranar 12 ga Yuni, 2025, yayin da suke hanyarsu domin halartar daurin auren dan uwansu.

‘Yan sanda sun gurfanar da mutanen 20 a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda hudu da suka haɗa da, hada baki wajen aikata laifi, amfani da makamai masu hatsari, halaka wasu da kuma jikkata mutane da gangan.

Tun da farko, a watan Yuli, lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhumar sun nemi kotu ta ba su beli amma ba su samu ba saboda kotun ta shiga hutu,hakan ya sa aka dage sauraren shari’ar zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2025.

Sai dai a ranar 14 ga Agusta, 2025, mai shari’a Musa ya amince da bukatar belin bayan karɓar ƙarar da aka gabatar a ranar 11 ga Agusta daga lauyan mutanen da ake tuhuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara