Mukaddashin Gwamnan Jihar Katsina, Farouk Lawal Jobe, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta ɗaukar matakai na musamman wajen kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da suka ƙara ta’azzara a jihar.
Wannan roƙo na zuwa ne bayan wani mummunar harin da aka kai wa al’ummar Mantau, karamar hukumar Malumfashi, inda ’yan bindiga suka kashe mutane 13 a masallaci yayin da suke salla da safiyar Talata.
A cewar Jobe, hare-haren sun fi yawa musamman a lokacin damina, abin da ke bai wa ’yan ta’adda damar fakewa cikin dazuzzuka suna kai farmaki kan manoma da mazauna yankunan.
Ya ce akwai buƙatar Shugaban Ƙasa ya ba hukumomin tsaro umarnin kai tsaye domin kawo ƙarshen wannan barazana.



