Jam’iyyar PDP ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ta nemi a tsige wasu ‘yan majalisa hudu daga Osun da ke majalisar dokoki ta saboda sauya sheƙa zuwa APC.
Lauyan jam’iyyar PDP, Rapheal Oyewole, ne ya shigar da ƙara gaban kotu a ranar 20 ga watan Agusta, 2025.
Ƴan majalisar da ake nema a tsige su sun haɗa da,
Sanata Francis Fadahunsi (Osun East),Sanata Olubiyi Oluwole Fadeyi (Osun Central),Hon. Omirin Olusanya (Atakumosa East/West da Ilesa East/West),Hon. Taofeek Ajilesoro (Ife Central/East/North da South)
PDP ta yi nuni da sashe na 68(1)(g) na kundin tsarin mulki na 1999, wanda ya haramta wa dan majalisa ci gaba da rike kujera idan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar da ya ci zabe a cikinta, sai dai idan ko jam’iyyar ta rushe.
Jam’iyyar ta nemi kotu ta bayar da umarnin cewa kujerun su sauka daga kan kujerun tun daga ranar da suka fice daga PDP.



